Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad ta kasar Lebanon an bayyan acewa, za agudanar da taron tunawa da shahidan kasar Turkiya da suka rasa rayukansu a yunkurinsu na kawo karshen killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar yankin.
Taron za a gudanar da shi ne da nufin raya ruhin taimako tsakanin dukkanin al'ummomin duniya, musamman ma wadanda suka samu kansu cikin kangizn zalunci da daniyar da ke samun kariya kai tsaye daga kasashen duniya masu girman kai.
Ya ci gaba da cewa yanzu haka al'ummomin duniya sun farga daga gudanar da taron tunawa da shahidan kasar Turkiya da suka rasa rayukansu a yunkurinsu na kawo karshen killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi a kan palastinawa.
718615