Bangaren kasa da kasa;A ranar ashirin da biyar ga wannan wata na Dai shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar da taron karawa juna ilimi kan fassarar suratul Hadid a jami'ar birnin London na Birtaniya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta IIDR ya watsa rahoton cewa; A ranar ashirin da biyar ga wannan wata na Dai shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar da taron karawa juna ilimi kan fassarar suratul Hadid a jami'ar birnin London ta Birtaniya. Wannan taro za a fara gudanar da shi ne da misalin karfe tara na safe har zuwa karfe shidda da rabi na marece agogon kasar Birtaniya inda za a yi bayani dalla-dalla kan bangarori da suratul Hadid din ta kumsa.
718673