IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Musulunci,Sulhu Da Adalci A Indonosiya

15:20 - December 28, 2010
Lambar Labari: 2054993
Bangaren siyasa da zamantakewa: taron kasa da kasa mai taken Musulunci,sulhu da adalci na kasa da kasa da za a gudanar a Indonosiya da hukumar Musulunci Muhammadiya tare da hadin guiwa da ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a Indonosiya a watan Isfand na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron kasa da kasa mai taken Musulunci,sulhu da adalci na kasa da kasa da za a gudanar a Indonosiya da hukumar Musulunci Muhammadiya tare da hadin guiwa da ofishin yada al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran a Indonosiya a watan Isfand na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.Mahmud Farazande jakadan jamhuriyar Musulunci ta Iran da Muhammad Ali Rabani mai kula da ofishin yada al'adun Iran a Jakarta da kuma Dine Shamsul Dine shugaban hukumar Musulunci ta Muhammadiya sun tattaunawa a tsakaninsu kan wannan taro karo na biyu.

719111

captcha