Bangaren kasa da kasa, An bude wani sabon reshe na babban bankin muslunci na duniya a birnin Abudhabi fadar mulkin kasar hadaddiyar daular larabawa da nufin fadada dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen musulmi bisa koyarawa irin ta addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, tawagar karya killace yankin zirin Gaza ta kasashen nahiyar Asia ta bi ta yankin Lazikiyya na kasar Syria domin isa yankin zirin da haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da killacewa da nufin takurawa al'ummar yankin.
Wannan tawaga ta bar yankin Lazikiya tun a yammacin jiya da nufin isa kasar, inda daga can za su kama zuwa yankin Rafah inda za su bi ta mashigar Rafah wadda ita ce babbar mashigar yankin zuwa zirin Gaza. Da dama daga cikin mutanen da ke cikin tawagar dai sun sha alwashin jurewa duk wata wahala da za su iya fuskanta kan hakan.
Tun a cikin makon da ya gabata ne gwamnatin ta dauki matakin rufe mashigar rafah, tare da hana wasu daga cikin mutanen da suke cikin tawagar takardun izinin shiga cikin kasarta Masar ta dauki matakin rufe mashigar rafah, tare da hana wasu daga cikin mutanen da suke cikin tawagar takardun izinin shiga ciki.
719123