Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na reshensa da ke kasar Laban cewa, tawagar manema labarai na kasar Iran da suke gudanar da ziyarar aiki a kasar sun ziyarci babban ofishin tashar lalabijin ta Almanar da ke birnin Beirut fadar mulkin kasar mallakin kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah.
Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin zirar ganewa ido da suke gudanarwa, iraniyawan manema labarai sun gana da jami'an tashar talabijin ta Almanar, inda suka kara samun haske dangane da shirye-shiryen da tashar take gudanarwa, da kuma yadda take kara samun ci gaba a cikin ayyukanta.
Tashar talabijin Almanar mallakin kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah tana daya daga cikin tashoshin talabijin na larabawa da ke bayyana hakikanin abin da yake faruwa na zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar palastinu.
720218