IQNA

13:02 - December 29, 2010
Lambar Labari: 2055559

An sanar Da Lokacin fara Gudanar Da Tarukan Cibiyar Musulunci Ta Tilmisan

Bangaren kasa da kasa, An sanar da lokacin fara gudanar da tarukan birnin Tilmisan bababr cibiyar musulunci da al'adunsa ta shekarar 2011, wanda za a gudanar a hukumance a kasar Aljeria tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar.




Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na El-watan an bayyana cewa, An sanar da lokacin fara gudanar da tarukan birnin Tilmisan bababr cibiyar musulunci da al'adunsa ta shekarar 2011, wanda za a gudanar a hukumance a kasar Aljeria tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Algeria.

Rahoton ya ci gaba da cewa Za a gudanar da zaman taron ne a matsayi na kasa da kasa, tare da halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Algeria da suka hada da shi kansa shugaban kasar Abdulaziz Butaflika, tare da ministoci da kuma mataimakansa.

A bangare guda kuma na bayyana cewa taron zai samu halartar wakilai daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da na musulmi da kuma na larabawa, da kuma wakilan kungiyoyi na kasa da kasa.

720071















captcha