IQNA

An Kafa Asusun Taimaka Ma Malaman Kur'ani Mai Tsarki A Makka

13:01 - December 29, 2010
Lambar Labari: 2055560
Bangaren kasa da kasa, An kafa wani asusun taimaka ma malamn kur'ani da suke horar da yara karatu da harda a birnin Makka mai alfarma, wanda Khalid faisal ya dauki nauyin kafawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Saudi Gazette an habarta cewa, an kafa wani asusun taimaka ma malamn kur'ani da suke horar da yara karatu da harda a birnin Makka mai alfarma, wanda Khalid faisal ya dauki nauyin kafawa da nufin tallafa musu.

Rahoton ya ci gaba da cewa kafin kafa wannan asusu an gudanar da tattaunawa tsakanin magajin garin birnin Makka mai alfarma Khalid Faisal da kuma mambobin kwamitin kula da ayyukan kur'ani na kasar, inda daga karshe aka amince da kafa wanann asusu.

Babbar manufar kafa wannan asusu dai ita ce samar da wata hanya ta samar da kudade domin gudanar da ayyukan da suka shafi kur'ani a cikin 'yanci da wadatar kudade, ta yadda malaman kur'ani za su iya yin kasafin kudaden da ake bukata.

719969




captcha