Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da wani shiri na koyar da wasu dalibai musulmi ma'anonin alkur'ani mai tsarki a kasar afirka ta kudu, wanda cibiyar nazari ta mutalat shariat islami ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, a birnin London na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na cibiyar nazarin muslunci ta kasar Afirka ta kudu an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na koyar da wasu dalibai musulmi ma'anonin alkur'ani mai tsarki a kasar afirka ta kudu, wanda cibiyar nazari ta mutalat shariat islami ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, a birnin Kape Town.
Za a fara gudanar da wannan shiri ne a farkon shekarar miladiyya ta 2011 a babban ofishin cibiyar da ke cikin birnin Kape Town, kuma wannan shiri zai kebanci kanan yara ne da kuma matasa musulmi na kasar, da nufin kara musu masaniya kan koyarwar kur'ani.
Yanzu haka dai an kamamla rijistar sunayen dukkanin yaran da za su shiga cikin wannan na bayar da horo, inda daruruwa daga cikinsu sun kammala dukkanin ayyukan rajistar, kuma suna jiran a kira su.
719859