Bangaren al'adu da fasaha: a ranar ashirin da takwas ga watan azar day a gabata na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin kano da ke arewacin kasar Nigeria aka gudanar da wani taro na al'adun Musulunci mai sunan muhimmacin sabon salo a manhajar koyarwa da reshen ofishin cibiyar yada addini ta duniya ta shirya.
Kamafanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne reshen Afrika na kamfanin ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Islamic-call ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da takwas ga watan azar da ya gabata na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a birnin kano da ke arewacin kasar Nigeria aka gudanar da wani taro na al'adun Musulunci mai sunan muhimmacin sabon salo a manhajar koyarwa da reshen ofishin cibiyar yada addini ta duniya ta shirya. Wannan zama daya daga cikin jerin tarurrukan da cibiyar za ta ci gaba da gudanarwa tare da malamai,masana da masu nazari da bincike da kuma malaman da ke koyar da harshen larabci da ke karkashin cibiyar yada addinin Musulunci.
720000