Bangaren nazari da ilimi;an tarjama littafin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a cikin littafi mai tsarki na kiristoci a cikin harshen Hausa.
Reshen Kamafanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Afrika ne ya watsa rahoton cewa: an tarjama littafin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka a cikin littafi mai tsarki na kiristoci a cikin harshen Hausa. Wannan littafi Ahmad Didad masani mai bincike musulmi dan kasar Afrika ta kudu ya rubuta shi a cikin harshen turancin Ingila yayin da Muhammad Sani Abubakar wani dan Nigeria ya tarjama shi a cikin harshen Hausa domin fayyacewa kirsitoci cewa labarin da siffofin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da layan gidansa ya z one a cikin littafin kiristoci kuma burin a biyu shi ne shafe mummunar fahima da farfaganda kan addinin Musulunci da tunani irin na maguzanci.
720290