Bangaren kasa da kasa, Babban kwamitin kula da ayyukan musulunci na kasar Lbanaon ya gudanar da tarukan girmama wasu daga manyan malaman addinin muslunci na kasar, babban malamin na mabiya mazhabar iyalan gidan manzo na kasar shi ne ya samu babbar girmamawa.
Kamafanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Nowlebanon ya watsa rahoton cewa: a ranar bakwai ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya Bahiya Hariri yan majalisar dokokin kasar Labanon ta bawa Ayatullahi AbdulmAmir Kablan mataimakin shugaban majalisar koli ta musulmi yan shi'a a kasar Labanon ta ba shi matsayi da kyautar jinjinawa ta kasa.
Wannan kyauta ta yabo da jinjinawa an bawa wannan malami nay an shi'a a daidai lokacin tunawa da yancin kasar ta Labanon inda ake bawa mutanan da suka yi fice ta fuskar hadin kai a kasar ta Labanon da kuma suke ta kara kokarin hada kai da tabbatar da sulhu a tsakanin yan kasar ta Labanon.
Malamin dai ya shahara wajen kokarin ganin an samu hadin kai mai dorewa tsakanin dukkanin alummomin kasar ta Labanon, da suka hada musulmi da dukkanin bangarorinsu, da kuma bangaren kiristoci da suke a kasar.
721523