Bangaren siyasa, Babban hankoron makiya muslunci shi ne samar da baraka mai zurfi da rashin fahimta mai tsanani takanin dukkanin bangarorin musulmi na duniya, ta hanyar yin amfani da wasu daga cikin musulmin da ba su fahimci addini ba, wanda hakan babban aibi ga musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya hbarta cewa, a wani bayani da yasamu daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almadina da ake bugawa a kasar Saudiyya an bayyana cewa, a rana ta biyu da aka shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa kasa da kasa da ake gudanarwa a Saudiyya mutane talatin ne suka yi saura, inda suke karawa da juna a rana ta biyu da aka shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa kasa da kasa da ake gudanarwa a Saudiyya mutane talatin ne suka yi saura, inda suke karawa da juna a karshen gasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin mutanen talatin suna karawa da juna ne a bangarorin karatu da harda da kuma ilmin tajwidi gami da sauran ilmomin kur'ani da suka hada da tafsiri, gami da dalilan safkar ayoyi, wanda daga cikinsu ne za a zabi matakai na farako da na biyu da na uku.
Gasar dai tana samun halartar mutane daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma kasashen musulmi da na larabawa, kuma an shiga kwanaki na 32 ne da fara gudanar da gasar.
721439