IQNA

An Buga Tare Da Yada Littafin Musulunci Da Kuma So A Syria

Bangaren al’adu, An buga tare da fitar da littafin nan mai suna musulunci da kuma so a cikin harshen larabaci a birnin Demacus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma wasu kasashen larabawa.
Kamfanin dillancinlabaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren sadarwa na kamfanin dillancon labaran kasar syria a yanar gizo an bayyana cewa, an buga tare da fitar da littafin nan mai suna musulunci da kuma so a cikin harshen larabaci a birnin Demacus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma wasu kasashen larabawa da kuma wasu kasashen Asia.

Bayanin ya kara da cewa babbar manufar buga littafin dai ita ce kara fitar da ma’anoni na so tsakanin al’ummomin duniya bisa mahanga ta addinin muslunci, an buga tare da fitar da littafin nan mai suna musulunci da kuma so a cikin harshen larabaci a birnin Demacus fadar mulkin kasar Syria tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar.

Yanzu haka dai littafin an kammala rarraba shi a dukkanin kasuwannin littafai da ke cikin birnin Damascus, kuma cibiyoyin buga littafai da dama na kasashen musulmi sun bukaci kwafi-kwafi na litatfin domin sayar da ga masu bukatar karantawa.

721340