IQNA

Gabatar Da Shawar Daukar Matakan Hana Kyamar Musulmi A Switzerland

11:43 - January 02, 2011
Lambar Labari: 2057209
Bangaren kasa da kasa, Wata cibiya mai zaman kanta mai suna kurtaba ta shirya gabatar da wasu shawarwari ga gwamnatin kasar Switzerland, domin shawo kan matsalar kyamar musulmi da ke karuwa a kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an bayyana cewa, wata cibiya mai zaman kanta mai suna kurtaba ta shirya gabatar da wasu shawarwari ga gwamnatin kasar Switzerland, domin shawo kan matsalar kyamar musulmi da ke karuwa a kasar ta Switzerland.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shawar tana kunshi ne da wasu muhimman abubuwan, da ya kamata gwamnatin wata cibiya mai zaman kanta mai suna kurtaba ta shirya gabatar da wasu shawarwari ga gwamnatin kasar Switzerland, domin shawo kan matsalar kyamar musulmi da ke karuwa.

Al'ummomin kasashen yammacin turai sun kara tsananta kiyayya ga Musulunci sakamakon bulluwar wasu kungiyoyi da jam'iyu masu adawa da Musulunci a kasashen, tun bayan kai harin sha daya ga watan satumba.

721826



captcha