IQNA

Jamhi’ar Azhar Ta Yi Alladawai Da Kai Harin Bam A Iskandariya

15:36 - January 03, 2011
Lambar Labari: 2058203
Bnagaren kasa da kasa, Jami’ar Azhar da ke birnin Alakhira fadar mulkin kasar Masar ta yi Allawadai da harin bam da ak ayi a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar miladiyya.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrwa na yanar gizo na Casafree an bayyana cewa, Jami’ar Azhar da ke birnin Alakhira fadar mulkin kasar Masar ta yi Allawadai da harin bam da ak ayi a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar miladiyya ta wannan shekara.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suke da hannu wajen shiryawa da kai wannan hari ba su wakiltar musulmin kasar masar da ma sauran musulmi na duniya baki daya, kuma babbar manufarsu ita ce samar da baraka da rashin fahimtar juna tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista da suke zaman lafiya.
An kai harin ne a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar miladiyya, lamarin da ya jawo ba ta kashi tsakanin jami’an tsaro da kuma mabiya addinin kirista bayan da suka mayar da martani kan wani masallaci.
722756





captcha