IQNA

An Shiga Bangaren Karshe Na Gasar Kur’ani A kasar Qatar

15:37 - January 03, 2011
Lambar Labari: 2058205
Bangaren kasa da kasa, An shiga bangaren karshe na gasar harda da karatun kur’ani mai tsarki ta sheikh Sheikh Ganim da ake gudanarwa akasar Qatar, wadda aka fara gudanarwa tun a cikin watan da ya gabata, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-sharq ta kasar Qatar an bayyana cewa, an shiga bangaren karshe na gasar harda da karatun kur’ani mai tsarki ta sheikh Sheikh Ganim da ake gudanarwa akasar Qatar, wadda aka fara gudanarwa tun a cikin watan da ya gabata, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar ta Qatar.
Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a sassa na harda da kuma tilawa gami da ilmin sanin kaidojin karatun kur’ani wato tajwidi, haka nan kuma na kasa gasar zuwa bangarori na farko na biyu da kuma na uku, da hakan ya hada da bayar da dama ga masu harda daga juzui na farko zuwa 20, daga nan zuwa sama.

Shiga bangaren karshe na gasar harda da karatun kur’ani mai tsarki ta sheikh Sheikh Ganim da ake gudanarwa akasar Qatar, wadda aka fara gudanarwa tun a cikin watan da ya gabata, tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa daban-daban na kasar wadda ta saba daukar gasar kur’ani.
722724


captcha