IQNA

Limamin Juma’a A Katif Ya Yi Kakkausar Suka Kan Fitar Da Wani Malami A Saudiyya

15:36 - January 03, 2011
Lambar Labari: 2058207
Bangaren kasa da kasa, Babban malamin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a yankin Katif na kasar Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya yi kakkausar suka kan fitar wani malami mabiyin mazhabar iayalan gidan manzo da aka yi daga wurin aikinsa bayan ya koyar da sallah daidai da koyarwar mazhabar ahlul bait.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid cewa, babban malamin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a yankin Katif na kasar Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya yi kakkausar suka kan fitar wani malami mabiyin mazhabar iayalan gidan manzo da aka yi daga wurin aikinsa bayan ya koyar da sallah daidai da koyarwar mazhabar ahlul bait ga wasu daga cikin dalibai da suka nemi sanin hakan.
Sheikh Saffar ya bayyana matakin da mahukuntan kasar Saudiyya suka dauka kan wannan bawan Allah da cewa ba mataki na adalci ba, kuma wannan ba shi ne karon farko da mahukuntan saudiyya da ke bin tafarkin wahabiyanci kan koyarawar mazhabar Ibn Tamiyya suke fara yin hakan kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah ba.
Babban malamin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a yankin Katif na kasar Saudiyya Sheikh Hassan Saffar ya yi kakkausar suka kan fitar wani malami mabiyin mazhabar iayalan gidan manzo da aka yi daga wurin aikinsa bayan ya koyar da sallah daidai da koyarwar shi’a

722660

captcha