Bangaren kasa da kasa, Babban ofishin kungiyar hadin kan musulmi ta OIC da ke birnin Alakhira fadar mulkin kasar Masar ya yi Allawadai da harin bam da aka yi a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar bana.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrwa na yanar gizo na Casafree an bayyana cewa, Ofishin OIC da Jami’ar Azhar da ke birnin Alakhira fadar mulkin kasar Masar sun yi Allawadai da harin bam da aka yi a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar miladiyya ta wannan shekara ta miladiyya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suke da hannu wajen shiryawa da kai wannan hari ba su wakiltar musulmin kasar masar da ma sauran musulmi na duniya baki daya, kuma babbar manufarsu ita ce samar da baraka da rashin fahimtar juna tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista da suke zaman lafiya da fahimtar juna.
An kai harin ne a birnin Iskandariya a kan mabiya addinin kirista a lokacin da suke tarukan murnar shiga sabuwa shekarar miladiyya, lamarin da ya jawo ba ta kashi tsakanin jami’an tsaro da kuma mabiya addinin kirista bayan da suka mayar da martani kan wani masallaci da ke kusa.
722756