BangarenA’adu da fasaha, An buga tare da yada wani littafi da yake dauke bayani mai zurfi kan hakikanin waki’ar Karbala a cikin harshen faransanci, domin amfani ma’abuta harshe da kuma wadanda suke fahimtarsa a cikin kasashen turai da sauran kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na harkokin kur’ani da yada al’adun musulunci nun an bayyana cewa, an buga tare da yada wani littafi da yake dauke bayani mai zurfi kan hakikanin waki’ar Karbala a cikin harshen faransanci, domin amfani ma’abuta harshe da kuma wadanda suke fahimtarsa a cikin kasashen turai da sauran kasashen duniya daban-daban.
Wanda ya jagoranci ayyukan buga tare da littafin Sabah Talikani ya bayyana cewa babbar manufar yin hakan ita ce samar da wani yanayi na wayar da kan al’ummomin duniya kan hakikanin abin da ya faru da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a karkashin jagorancin Imam Hussain (AS) a Karbala.
Ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu an kammala ayyukan buga littafin baki daya, an kuma fara aikewa da kwafi-kwafinsa zuwa wasu cibiyoyi na yada ilimi da al’adu na kasa da kasa, da ke cikin kasashen musulmi da kuma kasashen turai da na Asia.
722362