IQNA

Hada Karfi Da Karfe Shi Zai Kawo Karshen Barazana Ga Musulmi

18:21 - January 03, 2011
Lambar Labari: 2058276
Bangaren siyasa da zamantakewa, Majalisar musulmin kasar Faransa ta kirayi dukkanin musulmi zuwa ga hadin kai domin shiga kafar wando daya da ayyukan ta’addanci a fadin duniya, tare yin Allawadai da dukkanin ayyukan ta’addancin da ake aikatawa da sunan addinin muslunci a cikin kasashen musulmi da kasashen da ba na musulmi ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lecfcm cewa, majalisar musulmin kasar Faransa ta kirayi dukkanin musulmi zuwa ga hadin kai domin shiga kafar wando daya da ayyukan ta’addanci a fadin duniya, tare yin Allawadai da dukkanin ayyukan ta’addancin da ake aikatawa da sunan addinin muslunci a cikin kasashen musulmi da kasashen da ba na musulmi ba a fadin duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ayyukan ta’addanci da wasu suke aikatawa da sunan musulunci ba suna wakiltar musulmi ba ne ko addinin muslunci, kuma dole ne musulmi baki daya su tabbatar wa duniya da hakan, ta hanyar daukar matakan shiga kafar wando daya da masu aikata hakan.
Majalisar musulmin kasar Faransa ta kirayi dukkanin musulmi zuwa ga hadin kai domin shiga kafar wando daya da ayyukan ta’addanci a fadin duniya, tare yin Allawadai da dukkanin ayyukan ta’addancin da ake aikatawa da sunan addinin muslunci a cikin kasashen musulmi da sauran kasashe.
722686


captcha