IQNA

Tarukan Cika Shekaru Biyar Da Kai Hari Kan Hubbaren Imamai Biyu A Samirra

11:22 - January 04, 2011
Lambar Labari: 2058618
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da tarukan cika shekaru biyar da kai harin ta'addanci a kan hubbaren Imaman ahlul bait biyu (AS) da ke garin samirra a arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, tare da halartar malamai da kuma wasu jami'an gwamnati.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-dahr an bayyana cewa, an gudanar da tarukan cika shekaru biyar da kai harin ta'addanci a kan hubbaren Imaman ahlul bait biyu (AS) da ke garin samirra a arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki, tare da halartar malamai da kuma wasu jami'an gwamnatin kasar ta Iraki.

Bayanin ya ci gaba da cewa a lokacin gudanar da taron a jiya an gabatar da jawabai daga bakunan malamai da kuma jami'an gwamnati gami da wakilan cibiyoyin kare hakkin bil adama da addini da ke kasar Iraki, inda aka dora alhakin abin da ya faru a kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Masu jawabi sun bayyana manufar hakan da cewa ba komai ba ne illa hankoron haifar da fitina tsakanin mabiya tafarkin iayalan gidan manzon Allah da kuma 'yan sunna da ke zaune a kasar.

723490



captcha