Bangaren kasa da kasa, Tawagar kungiyoyin kare hakkin bil adama da lauyoyi da wakilan kungiyoyi likitoci da na bayar da agaji na kasashen Asia ta isa yankin zirin Gaza ta ashigar Rafah da ke kasar Masar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Kuna an habarta cewa, tawagar kungiyoyin kare hakkin bil adama da lauyoyi da wakilan kungiyoyi likitoci da na bayar da agaji na kasashen Asia ta isa yankin zirin Gaza ta ashigar Rafah da ke kasar Masar da nufin karya takunkumi da kuma killacewar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa al'ummar yankin marassa kariya.
Wanann tawaga dai tana dauke da kayayyakin taimako da suka hada da kayan abinci, magunguna, tufafi da dai sauran kayayyaki da al'ummar yankin ke bukata domin ci gaba da rayuwa kamar sauran mutanen duniya.
Gwamnatin kasar masar tare da hadin baki da haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana wasu daga cikin mutanen da ke cikin tawagar izinin shiga cikin kasarta, yayin da ta hana wasu shiga cikin yankin Gaza ta mashigar Rafah.
723466