Bangaren kasa da kasa, Babbar majalisar musulmin kasar Faransa za ta gudanar da zamanta a matsayi na ashirin da shida,domin yin bitar muhumman ayyukan da ta gudanar a cikin shekara da kuma sauran shekaru da suka gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na pageshalal cewa, babbar majalisar musulmin kasar Faransa za ta gudanar da zamanta a matsayi na ashirin da shida,domin yin bitar muhumman ayyukan da ta gudanar a cikin shekara da kuma sauran shekaru da suka gabata tun bayan kafa kungiyar.
Cibiyar mafi girma da ke kula da ayyukan muslunci ta birnin Lyon ce ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan zaman taro, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar farnsa da kewaye.
Babban sakataren cibiyar ya bayayna cewa manufar gudanar da wannan zaman taro dai tana da dangantaka ne kai tsaye da muhimmancin koyarwar manzon Allah ga musulmi da ke da imani sa dakon manzo.
723270