Bangaren kasa da kasa, An zabi birnin Ashraf a matsayin birnin al'adun muslunci a cikin shekara ta 2012, wanda kungiyar hadin kasashen musulmi ta duniya ta sanar, kuma yanzu hakan birnin ya fara shirin daukar bakuncin tarukan da za a gudanar a cikin shekara mai zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aswatul iraq cewa, an zabi birnin Ashraf a matsayin birnin al'adun muslunci a cikin shekara ta 2012, wanda kungiyar hadin kasashen musulmi ta duniya ta sanar, kuma yanzu hakan birnin ya fara shirin daukar bakuncin tarukan da za a gudanar a cikin shekara mai zuwa ta 2012.
Babban daraktan ma'aikatar raya aladu ta kasar Iraki ya bayyana cewa yanzu haka sun kafa wani kwamiti na yin bitar muhimamn abubuwan da ya kamata a mayar da hankali kansu kafin lokacin gudaar da zaman taron a cikin shekara mai zuwa.
Birnin najaf Ashraf dai shi ne babban birnin na yada ilmin mazhabar iyalan gidan manzon Allah, wanda ya samar da manyan malamai da duniya take alfahari da su a wannan bangare.
723243