Bangaren kasa da kasa, Kwamitin shawara na kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a ciki yake kiran dukkanin masu bin addinai da aka safkar daga sama da su hada kai domin shiga kafar wando daya da masu tsatsauran ra'ayi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, wamitin shawara na kasashen musulmi ya fitar da wani bayani da a ciki yake kiran dukkanin masu bin addinai da aka safkar daga sama da su hada kai domin shiga kafar wando daya da masu tsatsauran ra'ayi.
Rahoton ya kara da cewa babbar manufar kafa wanna kwamiti ita ce haifar da yanayi na zaman lafiya da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula tsakanin mabiya addinan biyu, musamman ma a cikin 'yan lokutanan, lamarin da ya fuskanci Allawadai daga malaman addinin muslunci da kungiyoyi.
A cikin watan decemban da ya gabata an kai wasu hare-hare kan majami'oin mabiya addinin kirista a Masar, kamar yadda aka kai wasu makamantansu a lokacin da suke bukin sabuwar shekarar bana.
723181