IQNA

An Bayar Da Lambar Yabo Ta Kasar Faransa Ga Shugaban Majalisar Musulmin Kasar

14:07 - January 05, 2011
Lambar Labari: 2059547
Bangaren kasa da kasa, An bayar da lambar yabo ta kasar faransa ga shugaban majalisar musulmin kasar Muhammad Musawi, saboda kokarin da yake yi na ganin an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da kuma sauran mabiya addinai na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, An bayar da lambar yabo ta kasar faransa ga shugaban majalisar musulmin kasar Muhammad Musawi, saboda kokarin da yake yi na ganin an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da kuma sauran mabiya addinai na kasar baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa ana bayar da wannan lambar girma ne ga mutumin da ya taka gagarumar rawa a wani fage, wadda ake kira kyautar Shawali ta kasa, wadda ake bayarwa tun lokacin mulkin sarakunan faransa a cikin shekara ta 1802. Daga cikin sharuddan bayar da kyautar har da yin hidima ta shekaru akalla 20 zuwa 25 abin da ya yi sama.
Bayar da lambar yabo ta kasar faransa ga shugaban majalisar musulmin kasar Muhammad Musawi, saboda kokarin da yake yi na ganin an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da kuma sauran mabiya addinai na kasar babban dalili ne kan irin rawar da musulmi suke takawa a fagen zaman lafiya.
724126



captcha