Bangaren kasa da kasa, Cibiyoyin addinin muslunci na kasar Faransa sun tabbatar da cewa gudanar da tarukan da suke yi a sassa daban-daban na kasar na da matukar tasiri wajen wayar da kan masana da kuma hattama ‘yan siyasa gami da sauran mutane a kasar, fiye da lokutan da suka gabata da babu wani mai kama da hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na pageshala an bayyana cewa, Cibiyoyin addinin muslunci na kasar Faransa sun tabbatar da cewa gudanar da tarukan da suke yi a sassa daban-daban na kasar na da matukar tasiri wajen wayar da kan masana da kuma hattama ‘yan siyasa gami da sauran mutane a kasar, fiye da lokutan da suka gabata da babu wani mai kama da hakan daga ayyukan da suke gabatarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa ana bayar da wata lambar girma ne ga mutumin da ya taka gagarumar rawa a wani fage, wadda ake kira kyautar Shawali ta kasa, wadda ake bayarwa tun lokacin mulkin sarakunan faransa a cikin shekara ta 1802. Daga cikin sharuddan bayar da kyautar har da yin hidima ta shekaru akalla 20 zuwa 25 abin da ya yi sama.
Bayar da lambar yabo ta kasar faransa ga shugaban majalisar musulmin kasar Muhammad Musawi, saboda kokarin da yake yi na ganin an samu zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin musulmi da kuma sauran mabiya addinai na kasar babban dalili ne kan irin rawar da musulmi suke takawa a fagen zaman lafiya da fahimtar juna.
724076