IQNA

Bayanin Majalisar 'Yan Shi'ar Bahrain Da Ke Goyon Bayan Jagoransu A kasar

11:47 - January 06, 2011
Lambar Labari: 2059853
Bangaren kasa da kasa, Majalisar malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahrain ta fitar da wani bayani da ke nuna cikakken goyon bayan ga babban malaminsu na kasar Ayatollah Isa Ahmad, tare da yin kakakusar suka ga masu cin zarafinsa daga wahabiyawan kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mabiya mazhabar shi'a cewa, ajalisar malaman mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahrain ta fitar da wani bayani da ke nuna cikakken goyon bayan ga babban malaminsu na kasar Ayatollah Isa Ahmad, tare da yin kakakusar suka ga masu cin zarafinsa daga wahabiyawan kasar ta Bahrain.

Rahoton ya kara da cewa babu wani dalili da zai sanya wahabiyawan kasar Bahrain su dauki kaean tsana su dora kan bababn malamin, wanda kuma shi ne ya fi kowa yawan mabiya a kasar ta Bahrain, wadda akasarin mutanenta mabiya mazhabar iyaan gidan amnzon Allah ne.

Bayanin ya ce dole mahukuntan kasar Bahrain su dauki matakin kawo karshen rarraba tsakanin dukkanin al'ummomin kasar, ba tare da nuna bangaranci kan goyon baya ko rashin goyon bayan wani bangare ba, kuma rashin hakan zai cutar da gwamnati ta dukkanin fuskoki.

724856











captcha