Bangaren kasa da kasa, Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah kimanin dubu goma sha biyar ne daga kasar Bahrain za su halarci tarukan cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala mai alfarma,
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ansar an bayyana cewa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah kimanin dubu goma sha biyar ne daga kasar Bahrain za su halarci tarukan cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala mai alfarma da ke cikin kasar Iraki.
Bayanin ya ci gaba da cewa tuni ofishin jakadancin kasar Bahrain da ke birnin Bagaza, da kuma karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Najaf suna shirinsu na tarbar dukkanin wadannan baki, da za su gudanar da ziyara ta makonni biyu a cikin kasar Iraki.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah kimanin dubu goma sha biyar ne daga kasar Bahrain za su halarci tarukan cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Hussain (AS) a hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala.
720768