IQNA

Za A Fara Gudanar Da Shirin Kyautata Rayuwar Limaman Masallatai A Morocco

11:15 - January 10, 2011
Lambar Labari: 2061931
Bangaren kasa da kasa, Za a fara aiwatar da wani shiri na daukar nauyin malaman addini tare da kyautata rayuwar liman masallatai na fadin kasar, wanda aka gabatar tun a cikin shekarun baya, kuma ake da shirin aiwatar da shi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an kamfanin dilalncin labaran kasar faransa an habarta cewa, za a fara aiwatar da wani shiri na daukar nauyin malaman addini tare da kyautata rayuwar liman masallatai na fadin kasar, wanda aka gabatar tun a cikin shekarun baya, kuma ake da shirin aiwatar da shi a cikin wannan shekara.

Wannan shiri an gabatar da shi ne da nufin mika shi ga ma'akatar kula da harkokin addini ta kasar, wanda ake jiran amincewarta kafin fara aiwatar da shi. shirin dai ya samu karbuwa da yin na'am daga manyan malamai da mabiya addinin musulunci na kasar.

A wata zantawa da ta hada ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar da manema labarai ya bayyana cewa, yanzu haka dai ana shirin ware makudan kudade da zasu kai yuro miliyan goam sha biyu domin aiwatar da wannan shiri a matakin farko.

726825





captcha