Banagaren kasa da kasa, Shirin samar da wata babbar cibiya ta yada ilmomin addinin muslucni ta hanayar yanar gizo a kasar Indonesia, wanda cibiyar yada ilimi ta Hauzar Amirul muminin ta birnin Jakarta tare da Hauzar birinin Qom da ke Iran suka dauki nauyin aiwatarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarnsa ke birnin Qom an bayyana cewa, shirin samar da wata babbar cibiya ta yada ilmomin addinin muslucni ta hanayar yanar gizo a kasar Indonesia, wanda cibiyar yada ilimi ta Hauzar Amirul muminin ta birnin Jakarta tare da Hauzar birinin Qom da ke Iran suka dauki nauyin aiwatarwa a cikin wannan shekara.
A zanatawar da ta hada kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna da daya daga cikin manyan jami'an da suke kula da harkokin ilmin na'ura mai kwakwalwa Alireza Ahmadlu ya bayyana cewa, yanzu dukkanin bangarorin biyu sun rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, wadda za ta amfanar da masu yin nazari kan addinin muslunci.
Tun a cikin shekara ta 2010 ne dukkanin bangarorin suka amince da su samar da wata hanya mafi sauki ta gudanar da bincike kan addini ta hanyar yanar gizo, ta yadda amsu bincike kan addinin muslunci za su samu saukin yin nazari.
726617