Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani babban taro na musulmin kasar Amurka a karo na goma sha biyu, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na sadarwa na ISNA an bayyana cewa, za a gudanar da wani babban taro na musulmin kasar Amurka a karo na goma sha biyu, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a jahar Ilnews.
Rahoton ya ci gaba da cewa wannan zaman taro akan shirya gudanar da shi a kowace shekara, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar Amurka, da suka hada malaman jami'a da kuma shugabannin cibiyoyin mulunci na jahohin kasar.
Gudanar da wani babban taro na musulmin kasar Amurka a karo na goma sha biyu, wanda cibiyar bunkasa harkokin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, na da matukar muhimmanci ga musulmin kasar Amurka.
726942