Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na news.in.msn cewa, babban malamin gwamnatin kasar Masar Sheikh Ahmad Juma'a ya kama hanyar isa kasar India domin halartar taron kasa da kasa kan musulunci a birnin New Delhi fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka wasu daga cikin manyan malaman addini daga kasashen duniya musamman na musulmi da na larabawa duk sun fara isa kasar ta India da nufin halartar wannan zaman taro na kasa da kasa, wanda zai yi dubi kan muhimmanci zaman lafiya tsakanin dukkanin addinai.
A yayin zaman taro manyan malamai da suka hada shugabannin cibiyoyin ilmin muslunci gami da shugabannin wasu daga cikin kasashen larabawa za su halarci zaman taron, haka nan kuma za su gana da mataimakin shugaban kasar ta India.
726978