Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wasu daga cikin yan kasashen waje musulmi a ganarawar da suka yi da shugabannin yankin Kurasan sun bukaci da su bada damar yan kasashen waje masu yawa damar saka jari a harkokin addini a Mashhad. A lokacin da suke tattaunawar da shugabannin yankin na Khurasan sun yi masu bayani dalla-dalla kan irin alfanon da ke tattare a cikin yin hakan da kuma irin nasarorin da za a cimma ta fuskar addini da zamantakewa da kuma tattalin arziki.
727136