IQNA

An Kama Babban Malamin Yan Shi'ar Azarbeijan

Bangaren siyasa da zamantakewa; a daren ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya yan sandan kasar Azarbeijan suka yi awangaba da Hujjatul Islam walmuslim Haj Zul Fakar Mika'il Zade babban malamin yan shi'ar wannan kasa.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin Kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a daren ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya yan sandan kasar Azarbeijan suka yi awangaba da Hujjatul Islam walmuslim Haj Zul Fakar Mika'il Zade babban malamin yan shi'ar wannan kasa. Wannan shekhul malamin yan shi'ar kasar ta Azarbeijan an yi awangaba da shi ne karkashin zargin dab a a bayyana ba kuma a na ci gaba da tsare da shi a ofishin yan sanda da ke Abshuran inda shugabannin da kungiyoyin addini na jamhuriyar azarbeijan sun yi babban taro da zaman dirshen a gaban ofishin yan sandan domin nuna adawa da kama shekhun malamin yan shi'ar kasar Mika'il.

727207