IQNA

Wani Malami a Najeriya:

Tozarta abubuwa masu tsarki barazana ce ga zaman tare a cikin al'umma

Abuja (IQNA) Wani malami  a Najeriya ya ce: ayyukan batanci irin na kur'ani mai tsarki a kasar Sweden rashin wayewa ne da kuma lalata zaman lafiya da zaman tare a tsakanin al'ummomi.
Musulman Denmark sun damu da kyamar Islama da kuma wulakanta wurare masu tsarki na Musulunci
Copenhagen (IQNA) Musulman kasar Denmark sun yi imanin cewa kona kur'ani a makwabciyar kasarsu Sweden abin bakin ciki ne,  Sun kuma damu da yaduwar kyamar Islama a Denmark.
2023 Jul 09 , 14:07
Majalisar Dinkin Duniya: Ba za mu sauya matsayinmu na yin Allah wadai da harin Isra'ila a kan Jenin ba
New York (IQNA) Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa babban sakataren wannan kungiya ba zai ja da baya daga matsayinsa na yin Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai sansanin Jenin da kuma amfani da wuce gona da iri kan fararen hula ba.
2023 Jul 09 , 15:21
Shirin Trump na dawo da dokar hana musulmi tafiya Amurka
New York (IQNA) Donald Trump, tsohon shugaban kasar Amurka, ya sanar da cewa, idan aka sake zabensa, zai aiwatar da dokar da ta haramta tafiye-tafiyen 'yan kasashen musulmi da dama kuma da tsananin tsanani.
2023 Jul 08 , 15:19
Martanin Ikea ga barazanar kauracewar musulmi
Bayan kona Alkur'ani a kasar Sweden;
Rabat (IQNA) Kamfanin Ikea na kasar Sweden, reshen Morocco, ya sanar da cewa an wanke shi daga kona kur’ani a kasar Sweden, saboda fargabar takunkumin da kasashen musulmi suka dauka.
2023 Jul 08 , 14:21
Falastinawa biyu sun yi shahada uku sun jikkata sakamakon harin da sojojin yahudawan sahyoniyawan suka kai kan Nablus
Ramallah (IQNA) Bayan harin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai a tsohon yankin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan da kewaye a safiyar yau 16 ga watan Yuli wasu matasan Palastinawa biyu sun yi shahada tare da jikkata wasu uku na daban.
2023 Jul 07 , 18:27
Jaridar Sweden: Sweden na neman sanya Kona kur’ani a matsayin aiki na laifi
Stockholm (IQNA) A ranar Alhamis, a wani rahoto da wata jaridar kasar Sweden ta ruwaito, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana yiwuwar mayar da kona kur'ani a kasar a matsayin aikin da ya sabawa doka.
2023 Jul 07 , 17:14
Matakin baya-bayan nan da kasar Iraki ta dauka kan wadanda suka tozarta kur'ani a Sweden
Baghdad (IQNA) Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki Ahmad al-Sahaf ya bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi maraba da gayyatar da Irakin ta yi masa na karbar bakuncin wani taron gaggawa kan lamarin kona kur'ani a kasar Sweden. Har ila yau, a cikin wani hukunci, babban mai shigar da kara na kasar Iraki ya ba da umarnin kame "Salvan Momika", wanda ya ci zarafin kur'ani mai tsarki a kasar Sweden.
2023 Jul 06 , 21:54
Gargadin kungiyar Hizbullah ta Lebanon game da yunkurin Tel Aviv mai hadari
Beirut (IQNA) A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar ta yi gargadi kan yunkurin da gwamnatin sahyoniyawan ke yi a yankin kauyen Al-Ghajar da ke kan iyakar kasar da Palastinu da ta mamaye.
2023 Jul 06 , 14:41
Martanin Biden a makare  game da wulakanta Al-Qur'ani
Washington (IQNA) Yayin ganawarsa da firaministan kasar Sweden da kuma mayar da martani kan wulakanta kur'ani a kasar Sweden, shugaban na Amurka ya ki yin Allah wadai da abin da ya faru.
2023 Jul 06 , 14:32
Keta alfarmar alamomin al'ummai ya yi nisa da ‘yan adamtaka
Babban malamin Kirista a Lebanon a wata hira da IQNA:
Beirut: Shahararren limamin kirista a kasar Labanon kuma shugaban sashen yada labarai na majalisar majami'u na gabas ta tsakiya ya jaddada cewa wulakanta tsarkakar addini, kasa da dabi'u na al'ummomi, ba tare da la'akari da ko akwai dokokin da za su hana hakan ba, dabi'a ce mai nisa daga bil'adama.
2023 Jul 06 , 14:05
Dan Jarida Bature: Kun ji kunyata kun kona littafi mafi girma a duniya
Landan (IQNA) Wani dan jaridan kasar Ingila yayi jawabi ga mahukuntan wannan kasa a zanga zangar nuna adawa da kona kur'ani a kasar Sweden tare da bayyana su a matsayin munafukai marasa kunya wadanda ba komai suke yi illa kare kalaman kyama na tsirarun masu tsatsauran ra'ayi da masu kiyayya.
2023 Jul 05 , 14:18
Dakarun mamaya na yahudawa sun sha kashi a Jenin a hannun Falastinawa ‘yan gwagwarmaya
Ramallah (IQNA) Bayan shafe kusan sa'o'i 48 ana kai hare-hare masu laifi kan sansanin Jenin, gwamnatin mamaya na Sahayoniya ta tilastawa yin gudun hijira daga wannan birni ba tare da cimma burinta ba.
2023 Jul 05 , 14:09