IQNA

Abul Ainain Ya Yi Tilawar Kur’ani Mai Tsarki A Kusa Da Hubbaren Imam Reda (AS)

15:58 - January 11, 2011
Lambar Labari: 2063004
Bangaren kasa da kasa, Shaharraen makarancin kur’anin nan na kasar Masar Abul’ainain ya gabatar da tilawar kur’ani mai tsarki a kusa da hubbaren Imam Reda (AS) da ke birnin Mashhad, wanda shi ne ake yi wa lakabi da shehin makaranta da mahardata na kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na lardin Khorasan ya habarta cewa, shaharraen makarancin kur’anin nan na kasar Masar Abul’ainain ya gabatar da tilawar kur’ani mai tsarki a kusa da hubbaren Imam Reda (AS) da ke birnin Mashhad, wanda shi ne ake yi wa lakabi da shehin makaranta da mahardata na kasar ta Masar, wadda ta shahara a duniya wajen yawan makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki.
Shehin malamin ya gabatar da tilawar ne a babban dakin taro na harabar hubbaren Imam Rida (AS) inda kuna a nan ne ake gudanar da taron gasar karatun kur’ani ma itsarki na kasa da kasaa birnin na mashhad, da ke samun halartar makaranta da mardata daga kasashen duniya arba’in da shida, musamman daga kasashen larabawa da na musulmi.
A lokacin da yake gabatar da karatun nasa bababn makarancin na kasar Masar, wakilin jagoran juyin juya halain muslunci a lardin Razavi tare da wasu jami’an lardin Khorasan sun samu halartar wurin gasar, wadda ake gudanarwa a karo na uku, a matsayin gasar daliban makarantu na kasashen musulmi.
727963

captcha