Bangaren kasa da kasa, An jaddada wajabcin kyautata yanayin masu ziyarar Imam Hussain (AS) a lokacin da ake gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da zagayowar lokacin shahadarsa, da ake gudanarwa hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala mai alfarma a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Brana na kasar Iraki an habarta cewa, limamin masallacin juma’a na birnin Bagadaza sheikh Jalaluddinin Sagir ya bayyana cewa, wajabi ne a kyautata yanayin masu ziyarar Imam Hussain (AS) a lokacin da ake gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da zagayowar lokacin shahadarsa, da ake gudanarwa hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya yi nuni da irin matsalolin da masu ziyara suke fuskanta a kasar Iraki, musamman a yankunan Kazimain inda ‘yan ta’adda suka fi kai hare-haren ta’addanci kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a lokacin da suke gudanar da ayyyukan ibada na ziyarar kabrukan limaman ahlul bait (AS)
wajabcin kyautata yanayin masu ziyarar Imam Hussain (AS) a lokacin da ake gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da zagayowar lokacin shahadarsa, da ake gudanarwa hubbarensa mai tsarki da ke garin Karbala mai alfarma da ke kasar.
727861