IQNA

Zaman Taro Kan kare Martabar Kur’ani Mai Tsarki A Birnin Jeneva

18:10 - January 11, 2011
Lambar Labari: 2063068
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma kare martabarsa a cikin kasashen duniya musamman ma a kasashen yamamcin turai, wanda za a gudanar a birnin Jeneva fadar mulkin kasar Switzerland.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cige an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma kare martabarsa a cikin kasashen duniya musamman ma a kasashen yamamcin turai, wanda za a gudanar a birnin Jeneva fadar mulkin kasar Switzerland, daya daga cikin mambobin kungiyar tarayyar turai.
Babbar cibiyar kula da harkokin musulmi da bunkasa koyarwa da ala’dun musulunci ta kasar tare da hadin gwiwa da kungiyar musulmin kasar Faransa bne suka dauki nauyin shiryawa da gudar da wannan zaman taro. Masannin nan na kasar faransa dakta Mustafa Ibrahimi shi ne wanda zai fara gabatar da jawabi a gaban taron.
Taron dai zai samu halaratr manyan malamaddinin muslunci daga kasashen musulmi da na larabawa, kamar yadda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na nahiyar turai, wadanda za su bayyana mahangarsu danagane da yadda wasu suka dauki addinin muslunci a cikin nahiyar.
Gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan matsayin kur’ani mai tsarki da kuma kare martabarsa a cikin kasashen duniya musamman ma a kasashen yamamcin turai, wanda za a gudanar a birnin Jeneva fadar mulkin kasar Switzerland na da muhimmancin gaske.

727883
captcha