IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Allawadai Da Haramtacciyar kasar Isra’ila

18:12 - January 11, 2011
Lambar Labari: 2063070
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar hadin kan kasshen larabawa ta yi Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila, dangane da ci gaba da nuna wariya da yin kisan kiyashi da take kan al’ummar palastinu, da kuma daukar sabbin matakan rusa wurare masu tsarki da suke cikin birnin Qods.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na KUNA na kasar Kuwait an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasshen larabawa ta yi Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila, dangane da ci gaba da nuna wariya da yin kisan kiyashi da take kan al’ummar palastinu, da kuma daukar sabbin matakan rusa wurare masu tsarki da suke cikin baitul muqaddas.
Tun bayan da kungiyar hadin kan kasashen larabawa tare da gwamnatin palastinawa a Ramallah suka mika kai bori ya hau ga Haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da yin wasan kura da su, da kuma nuna wa duniya wallensu, inda ta yi watsi da duk wani yunkurin wanzar da zaman lafiya da gwamnatin yahudawa.
Kungiyar hadin kan kasshen larabawa ta yi Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila, dangane da ci gaba da nuna wariya da yin kisan kiyashi da take kan al’ummar palastinu, da kuma daukar sabbin matakan rusa wurare masu tsarki da suke cikin birnin Qods mai alfarma.
Haka nan kumakungiyar ta nnemi goyon bayan kasashen yammacin turai kan matsa lamaba kan Isra’ila da ta dakatar da abin da take yi na cin zalun din palastinawa a Gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan a cikin kwanakin nan.

727677
captcha