Bangaren kasa da kasa, Za a nuna wani sabon bugun kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen turanci a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda ofishin bunkasa al'adun Musulunci na kasar Iran da ke birnin ya dauki nauiyin gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na an habarta cewa, za a nuna wani sabon bugun kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen turanci a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda ofishin bunkasa al'adun Musulunci na kasar Iran da ke birnin ya dauki nauiyin gudanarwa a cikin wannan mako.
Muhammad javad Gohari, wanda dan asalin kasar Iran ne kuma shahararen marubuci a kasar Birtaniya, shi ne wanda ya tarjama wannan kur'ani mai tsarki, wanda ya samu yabo daga dukkanin cibiyoyin Musulunci na kasar Birtaniya, bisa namijin kokarin da ya yin a fitar da ma'anoni a cikin hanya mai sauki da za a iya fahimta.
Nuna wannan sabon bugun kur'ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen turanci a birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya, wanda ofishin bunkasa al'adun Musulunci na kasar Iran da ke birnin ya dauki nauiyin gudanarwa, zai taimaka wajen kara fitowa da matsayin littafin mai tsarki ga al'ummar kasar.
729253