IQNA

An Yi Kakkausar Kan Buga Wani Littafi Mai Suna Mazhabar Shi’a A Nahiyar Afirka

16:06 - January 15, 2011
Lambar Labari: 2064798
Bangaren kasa da kasa, Mataimakin shugaban majalisar malaman musulunci ta duniya ya yi kakakusar suka dangane da buga wani littafi mai suna shi’a a Afirka, wanda a cikinsa aka nuna matukar kiyayya ga mazhabar iualan gidan manzon Allah da mabiya wannan mazhaba sakamakon ci gaba da karbar mazhabar iyalan gidan manzo a kasashen nahiyar Afirka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren sadarwa na majalisar malaman muslunci ta duniya cewa, Mataimakin shugaban majalisar malaman musulunci ta duniya ya yi kakakusar suka dangane da buga wani littafi mai suna shi’a a Afirka, wanda a cikinsa aka nuna matukar kiyayya ga mazhabar iualan gidan manzon Allah da mabiya wannan mazhaba sakamakon ci gaba da karbar mazhabar iyalan gidan manzo a kasashen nahiyar Afirka, musamman ma arewacin nahiyar.
A cikin wasikar wadda ya aikewa shugaban majalisar Yusuf Kardawi, mataimakin shugaban majalisar ya bayyana cewa wadanda suka rubuta wannan littafi hakikanin gaskiya ba su da masaniya kan mazhabar iyalan gidan manzon Allah da kuma yadda take yaduwa a cikin kasashen nahiyar Afirka, a kan haka ne ma suke rubuta abin da suka ga dama saboda kiyayyarsu da wannan mazhaba.
Ya ci Gaba da cewa wasu da suke danganta cibiyoyin da suke gudanar d ayyukansu na mazhabar iyalan gidan manzo a Afirka da Iran, suna yin kuskure domin wasunsu ma ba ma kawai ba su da dangantaka da Iran ba, har ma suna da banbanci tunani kan lamurra da dama da Iran. 730142
captcha