IQNA

An Buga Tare Yada Wata Nasharar Musulunci A Kasar Holland A karon Farko

16:07 - January 15, 2011
Lambar Labari: 2064801
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da watsa wata nashrar musulunci a karon farko a kasar Holland, wadda take yin karin haske kan yadda musulmin kasar suke gudanar da harkokinsu da ayyukansu a kasar inda wani matashi mai suna Joseph Stephens ya dauki nauyin bugawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kasar Kuwait KUNA an bayyana cewa, An buga tare da watsa wata nashrar musulunci a karon farko a kasar Holland, wadda take yin karin haske kan yadda musulmin kasar suke gudanar da harkokinsu da ayyukansu a kasar inda wani matashi mai suna Joseph Stephens ya dauki nauyin bugawa, da nufin bayyana wa mutanen kasar matsayin musulmi kan lamurra da dama, maimakon yadda suke daukar musulmi da mummnan gani.
Bayanin ya ci gaba da ci gaba da cewa musulmin kasar Holland wadanda akasarinsu baki ne ‘yan kasashen waje da suke zaune a kasar tun tsawon shekaru, musamman ma daga kasashen Turkiya da kasashen larabawa da kuma wasu kasashen Afirka, sun fara fuskantar matsalolin nuna musu wariya da banbanci ne tun bayan kai harin satumba.
Daga bisani kuma an samu bulluwar wasu kungiyoyi na masu tsananin kiyya da musulunci ya kara saka su cikin wani mawuyacin hali a kasar, amma ta hanyar wayar da kan mutane za su iya samun gagarumar nasara.
730117

captcha