Bangaren kasa da kasa, An gabatar da wata shawara dangane da kara yawan kasafin kudin shekara ga bangaren ilmin makamarntun musulmi na kasar India, inda aka mika wannan daftari a gaban zaman kwamitin kula da kasafin kudi da shirya yadda za a aiwatar da shi a aikace na kasar India.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Outlookindia an bayyana cewa, An gabatar da wata shawara dangane da kara yawan kasafin kudin shekara ga bangaren ilmin makamarntun musulmi na kasar India, inda aka mika wannan daftari a gaban zaman kwamitin kula da kasafin kudi da shirya yadda za a aiwatar da shi a aikace na kasar.
A lokacin da aka mika wannan daftari wadanda suka halarci zaman taron sun bayyana cewa bisa la’akari da karuwar adadin musulmi a kasar India, dole a mayar da hankali wajen kara kyautata rayuwarsu ta hanar kara yawan kasafin kudin da ake musu a kowace shekara.
Babban abin da bayanin ya fi mayar da hankali a aknsa baya ga batun kyautata rayuwar musulmin kasar India ta fuskoki da dama har ma da batun ilmi wanda ya fi muhimmanci bayan kyautata lamarin rayuwarsu ta zamantakewa, samar musu da ayyukan yi da sauransu.
730096