IQNA

Allah Ya Yi Wa Ayatollah Sayyid Mohammad Ali Milani Rasuwa

20:05 - January 15, 2011
Lambar Labari: 2064863
Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi Ayatollah Sayyid Mohammad Milani rasuwa, daya daga cikin manyan malaman addinin musuunci da ake komawa zuwa gare su a birnin Najaf Alashraf, kuma an gudanar da janazarsa a birnin Mashhad mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Allah ya yi Ayatollah Sayyid Mohammad Milani rasuwa, daya daga cikin manyan malaman addinin musuunci da ake komawa zuwa gare su a birnin Najaf Alashraf, kuma an gudanar da janazarsa a birnin Mashhad mai alfarma tare da halartar dubban musulmi daga sassa daban-daban na kasar Iran da Iraki da ma wasu kasashen musulmi.
An gudanar da janazar malamin ne daga makarntar Imam Sadiq (AS) da ke cikin birnin Mashhad da ke kan titin Ayatollah Shirazi, daga nan kuma aka nufin hubbaren Imam Ali Bin Musa Al-rida (AS) inda aka rufe malamin a koshewarsa ta karshe, dubban musulmi sun nuna matukar kaduwa da rashin malamin.
Malamin na daya daga cikin malaman mabiya mazghabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da suka taka gagarumar rawa wajen yada ilmi da fikira ta tafrkin iyalan gidan manzon a fadin duniya, ta hanayar koyar da dubban dalibai da kuma rubuta tarin littafai na addinin muslunci a rayuwarsa.
730103



captcha