Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro na wayar da kai dangane da addinin muslunci a babban dakin taruka na jami'ar British Colombia, wanda hakan daya ne daga cikin muhimman ayyukan da kungiyoyin muslumin kasar Canada ke gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ubyssey cewa, aa a gudanar da wani zaman taro na wayar da kai dangane da addinin muslunci a babban dakin taruka na jami'ar British Colombia, wanda hakan daya ne daga cikin muhimman ayyukan da kungiyoyin muslumin kasar Canada ke gudanarwa a kowace shekara.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro da ake shirin gudanarwa zai samu halartar manayan malaman jami'oi daga sassa na kasar Canada, da kuma masana gami dam alai musulmi da kuma wakilan kungiyoyin musulmin kasar, inda za a gabatar da laccoci kan hakikanin koyarwar addinin musulunci dangane da rayuwar zamantakewa.
Gudanar da wani zaman taro na wayar da kai dangane da addinin muslunci a babban dakin taruka na jami'ar British Colombia, wanda hakan daya ne daga cikin muhimman ayyukan da kungiyoyin muslumin kasar Canada ke gudanarwa, na da matukar muhimmanci wajen wayar da kan mutane.
730533