Bangaren kasa da kasa; : Said Ahmad Safi wakilin ayatullahi Uzma Said Sistani a hudubar sallar juma'a a birnin Karbala a ranar ashirin da hudu da watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya jaddada cewa Iraki bukatar karfafawa da fadada dangantakarta da sauran kasashen duniya na duniyar musulmi.
Kamfanin dillacin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya bayan nakaltowa daga majiyar labarai ta Nun watsa rahoton cewa; Said Ahmad Safi wakilin ayatullahi Uzma Said Sistani a hudubar sallar juma'a a birnin Karbala a ranar ashirin da hudu da watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya jaddada cewa Iraki bukatar karfafawa da fadada dangantakarta da sauran kasashen duniya na duniyar musulmi. Wannan mataki nada matukar alfano da kuma nasara a tattare da shi musamman idan aka yi la'akari da halin da musulmi ke ciki a yausuna bukatar hada kai da fadada dangantaka a tsakaninsu ko shakka babu.
730367