Bangaren kasa da kasa, An fitar da wata sabuwar nashara ta majalisar malaman mabiya mazhabar shi'a a kasar Bahrain, wadda aka saka ma suna Al-ilmani, wadda aka buga a cikin harshen larabci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a na majalisar shura ta 'yan shi'a a kasar Bahrain cewa, an fitar da wata sabuwar nashara ta majalisar malaman mabiya mazhabar shi'a a kasar Bahrain, wadda aka saka ma suna Al-ilmani, wadda aka buga a cikin harshen larabci wanda shi ne harshen kasa.
A cikin wannan sabuwar nashara, majalisar malaman mabiya mazhabar shi'a ta kasar Bahrain ta yi kakkausar suka zargin da tsohon sakataren kasar Amurka Donel Ramsfield ya yi wa bababn malamin addinin muslunci a kasar Iraki Ayatollah Ozma Sayyid Ali Sistani, wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah ke komawa zuwa gare shi.
Haka nan kuma a cikin nasaharar an mika sakon ta'aziyya ga dukkanin musulmi na duniya dangane da rasuwar daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci na kasar Bahrain Sheikh Muhammad Ali Al-akkar, wanda Allah ya yi wa rasuwa.
Majalisar malaman ta yi kakausar suka yadda wasu daga cikin jami'an kasashen ketare suke yi hawan kawara kan lamurran da suka shafi a ddinin muslunci musamman ma a kan malamai.
731181