IQNA

An Kai Hari Tare Da Kone Wasu Masallatai Kurmus A Kasar Bosnia

13:59 - January 17, 2011
Lambar Labari: 2066137
Bangaren kasa da kasa, Wasu bata gari da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari tare da kone wasu daga cikin masallatai a kasar Bosnia, da nufin haifar babban rikici tsakanin mabiya addinin muslunci da kiristocin kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA an bayyana cewa, Wasu bata gari da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari tare da kone wasu daga cikin masallatai a kasar Bosnia, da nufin haifar babban rikici tsakanin mabiya addinin muslunci da kiristocin kasar ta Bosnia.

Bayanin ya ci gaba da cewa Ministan harkokin cikin kasar shi ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa yanzu haka jami'an tsaro suna ci gaba da daukar tsauraran matakai da nufin gano duk wadanda suke da hannu a cikin wannan aika-aika, haka nan kuma ya sheda cewa ga dukkan alamu jam'iyun siyasar kasar ba su da wata dangantaka da abin day a faru.

Ya ce sasu bata gari ne da ba a san ko su wane ne ba suka kai harn tare da kone wasu daga cikin masallatai a kasar ta Bosnia, da nufin haifar babban rikici tsakanin mabiya addinin muslunci da kiristocin kasar, wanda ya ce hakan ba za ta faru ba.

731004






captcha