Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Hindustan Times an bayyana cewa, An gabatar da sabon canji dangane da gina babban masallacin birnin New York, wanda cibiyar musulunci ta birnin ta dauki nauyin ginawa domin samar da babbar cibiyar musulmin kasar Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu an canja daraktan gudanar da tsarin ginin masallacin, inda aka maye gurbinsa da Abdullah Azma a matsayin sabon daraktan aiwatar da sabon shiriin ginin babban masallacin na birnin New York.
An haifi AAbdullah Azma ne a birnin Washington, kuma ya kasace daya daga cikin musulmin kasar Amurka masu himmawaen gudanar da aikace-aikacen musulunci a kasar, inda ya jagoranci lamurran musunci da yawa.
Gabatar da sabon canji dangane da gina babban masallacin birnin New York, wanda cibiyar musulunci ta birnin ta dauki nauyin ginawa domin samar da babbar cibiyar musulmi, zai taiamak wajen kammala shirin.
730785